Labarai
Za mu hada kai da hukumomin kashe gobara don wayar da kan yan kasuwa- Shugabanni

Hukumar gudanarwar kasuwar sabon gari, ta ce za ta hada kai da hukumomin kashe gobara wajen wayar da kan yan kasuwa yadda za su magance tashin gobara.
Shugaban kasuwar ta sabon gari da Singa da kuma Galadima Alhaji Abdul Bashir Hussain, ne ya bayyana hakan yayin wata ziyara da hukumar kashe gobarar ta kai kasuwar.
Wata sanarwa da jami’in yada labaran kasuwar Sabon Gari Ado Haruna Muhammad, ya fiyar ta bayyana cewa, jami’an hukumar ta kashe gobara sun koyar da yan kasuwar yadda za su magance tashin gobara da kuma yadda za su kashe ta idan ta tashi kafin ta kai ga yin barna.
Haka kuma snarwar ta bayyana cewa, yayin ziyarar shugaban hukumar kashe gobara na Kano Alhaji Sani Anas, ya bukaci yan kasuwa da su mallaki kayayyakin kashe gobara wanda hakan ke daga cikin abinda ya zama dole ga kowanne dan kasuwa.
You must be logged in to post a comment Login