Labarai
Za mu kammala duk ayyukan Tituna da Gadoji a watan Disamban bana- Gwamnatin Kano

Gwamantin jihar Kano, ta sha alwashin kammala dukkan ayyukan tituna da gadoji da ta ke gudanar a fadin jihar nan da watan Disamban bana.
Kwamishina ayyuka Injiniya Marwan Ahmad ne ya bayyana hakan a zantawar sa da wakilinmu Nura Bello da safiyar yau Alhamis.
Injiniya Marwan Ahmad, ya kara da cewa nan gaba kadan gwamnatin Kano za ta kaddamar da sabbin ayyukan raya kasa a fadin jihar Kano.
You must be logged in to post a comment Login