Labarai
Za mu rufe asusun kafafen sada zumunta da ‘yan ta’adda ke tallata ayyukan su – Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa hukumomin tsaro na aiki tare da manyan kamfanonin kafafen sada zumunta a kasar domin gano tare da rufe asusun da ‘yan ta’adda da masu laifi ke amfani da su wajen tallata ayyukan su da tara kudi.
Babban Daraktan cibiyar yaki da ta’addanci na kasa Manjo Janar Adamu Laka ne, ya bayyana hakan a taron karshen shekara da ya gudana a birnin tarayya Abuja, inda ya ce ‘yan ta’adda na amfani da kafafe irin su TikTok, Facebook, Instagram, Snapchat da X wajen nuna hare-haren su.
Ya ce hukumomin tsaro sun yi tarurruka da dama da wadannan kamfanoni domin magance wallafe-wallafe da asusun da ke barazana ga tsaron kasa.
You must be logged in to post a comment Login