Labarai
Za mu samar da tsaro yayin bikin sallah shugabancin karamar hukumar birni
Shugabancin ƙaramar hukumar Birni na riƙo dake nan jihar Kano ya ce bayan karɓa wannan ƙaramar hukumar sun same ta cikin muhuyacin hali, kasancewar yadda sakatariyar take babu gyara babu kuɗi.
Shugaban karamar hukumar na riƙo Hon Bashir Baba Chilla ne ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da manema labarai a wani ɓangare na samarwa da ƙaramar hukumar Birni ci gaba.
Chilla ya kara da cewa sun sanya idanu kan ma’aikatan da suke aiki a wajen domin zuwa aiki akan lokaci da kuma gudanar da aiki yadda aka tanada domin sauke hakkin al’umma.
Akwai matsalar huta da wannan sakatariyar take fuskanta ta yadda a kullum takan zama babu huta sakamakon rashin kula da injin da yake bayar da huta,amma kawo wannan lokacin an samu gyara shi, inda yanzu haka huta ta samu a cikin sakatariyar, A cewar Chilla.
Akwai matsalar ƴan kilisa da wannan ƙaramar hukumar take fuskanta, adon haka ya zama wajibi shugabancin ƙaramar hukumar ya dau mataki domin kawo ƙarshen wannan ɓarna da ake yi a yayin hawan kilisar.
Haka kuma muna so musamar da kyakkyawan tsaro a ƙaramar hukumar shiyasa yanzu haka muka kafa wani kwamiti wanda zan sanya idon ko ta kwana musamman a wannan lokaci na ƙaratowar sallah karama.
Muna kira ga iyaye da su sanya idanu kan ƴaƴan su domin kaucewa rikice rikice da ake samu na yau da kullum a wannan ƙaramar hukumar.
Zamu tabbatar mun sanya idanu kan asibitocin mu da suke ƙaramar hukumar Birni domin bayar da kulawar lafiya ga dukkanin al’ummar da suke yankin ƙaramar hukumar.
Akwai tsarin da ƙaramar hukumar Birni tayi wajen bayar da tallafin abinci ga al’ummar ƙaramar hukumar ƙarkashin jagorancin gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf domin rage matsin rayuwa da al’umma suke ciki.
Hon Bashir Baba Chilla ya ce a wannan lokaci Ramadan an sami matsalar ciyarwa a wata santa da take ƙarƙashin sa wanda hakan baiyi daɗi ba kuma cikin ƙanƙanin lokaci aka sami canji, domin gudanar da abin da gwamnati ta tsara.
Ina kira ga al’umma duk abin da zasuyi su kasance sunyi abin su tsakanin su da Allah domin hakki ne da aka ɗorawa mu ku.
Domin wannan tsarin na ciyarwa a buƙatar ya isa ga kowa da kowa musamman bamuƙata da suke faɗin jihar nan.
You must be logged in to post a comment Login