Labarai
Za mu samarwa jihohin da ke fuskantar matsalar tsaro takin zamani – Buhari
Majalisar Zartarwa ta kasa ta amince da kashe Naira miliyan dari tara da ashirin da biyu da dubu dari takwas don sayen takin zamani da zai taimaka wa jihohin da ke fama da tashe-tashen hankula da kuma wadanda ibtila’in ambaliyar ya shafa tun daga shekarar 2018.
Ministar jin kai da kare abkuwar ibtila’i da ci gaban al’umma Hajiya Sadiya Umar Farouk ce ta bayyana hakan, lokacin da take yi wa manema labarai bayani a fadar Shugaban kasa a karshen taron Majalisar zartarwa.
Ta ce jihohin da za su ci gajiyar shirin sun hadar da Adamawa Borno da Yobe wadanda za su samu nau’ikan takin zamani a matsayin tallafi ga manoma.
A wani labarin kuma, ministan samar da hasken wutar lantarki Sale Mamman, ya bayyana cewa Majalisar ta amince da aiwatar da wasu manyan ayyuka guda biyu.
A cewar sa ayyukan sun hada da sayan tiransifomomi guda hudu a kan kudi naira biliyan uku da miliyan biyu don inganta samar da wutar lantarki a kasar nan.
Ya ce majalisar ta kuma amince da kashe naira miliyan dari da hamsin da biyar da dubu dari biyu don samar da mitar wuta miliyan daya a Oshodi da ke Jihar Legas, da Fatakwal da kuma Kaduna.
You must be logged in to post a comment Login