Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Za mu tabbatar ruwan fanfo ya isa ko ina a Kano- MD

Published

on

Zamu tabbatar ruwan fanfo ya isa ko ina a faɗin Kan.

Shugaban ma’aikatan jihar Kano Alh.Abdullahi Musa ya yi kira ga ma’aikatan hukumar samar da ruwa ta jihar Kano da su mayar da hankali wajen gudanar da ayyukansu.

Alhaji Abdullahi Musa ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya kai ziyarar ganin yadda aikin su yake wakana domin ƙara karfafa musu gwiwa.

Haka zalika shugaban ma’aikatan ya yabawa Manajan Daraktan hukumar Injiniya Garba Ahmad Bichi kan samar da ruwan sha ga sakatariyar Audu Bako cikin kankanin lokaci inda ya jaddada bukatar hukumar ta yi aiki tare da samar da wasu tsare-tsare na inganta samar da ruwan sha a jihar.

A nasa bangaren Manajan Daraktan Injiniya Garba Ahmad Bichi ya yi alkawarin sake rubanya ƙoƙarin samar da isasshen ruwa ga al’umma.

Injiniya Garba Bichi ya godewa shugaban ma’aikatan bisa wannan ziyarar da ya kawo masa tare da yi masa fatan alheri.

A wani labarin kuma Manajan Daraktan Hukumar Ruwa ta Jihar Kano Injiniya Garba Ahmad Bichi ya jaddada kudirin sa na tabbatar da samar da ruwan sha a jihar.

Injiniya Garba Bichi ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin jami’ar Yusif Maitama Sule a ofishinsa Ya yi alkawarin gyara matsalar da ke hana zuwan ruwa a sabon Jami’ar inda ya nuna godiya ga mahukuntan makarantar da suka kai rahoto ga hukumar.

Da yake jawabi tun da farko Farfesa Abubakar Salisu ya ce sun je ofishin MD ne domin neman taimakon hukumar ta samar da ruwan sha a jami’ar.

Farfesa Abubakar ya godewa Manajan Daraktan kuma ya yi alkawarin ba da hadin kai ga hukumar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!