Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Za mu tabbatar tallafin Dangote ya isa ga al’umma-Gwamna Abba

Published

on

Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya jagoranci kaddar da rabon tallafin kayan abinci da gidauniniyar Dangote zata rabawa al’ummar kasar nan.

Da yake kaddamar da rabon tallafin a gidan gwamnati, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya hori kwamitin da zasu gudanar da rabon abincin su zamo masu gaskiya da rikon amana tare da tabbatar da tallafin ya isa ga mabukatan da aka tanadi abincin dominsu.

Gwamna Abba Kabir Yusuf Wanda Yace tuni tallafin kayan abincin ya isa ga dukkanin kananan hukumomin jihar nan 44 Ya bayyana gamsuwarsa bisa tsarin da gidauniyar ta Dangote tayi na shigar da dakarun Hisba cikin tsarin wanda ya bayyana fatansa na cewa zasu tsaya Kan adalci da gaski yayin gudanar da rabon.

Ya godewa Alhaji Aliko Dangote bisa samar da wannan tallafi, musamman a wannan yanayi na tsadar rayuwa da ake fuskanta tare da yin Kira ga mawadata su yi koyi da irin wannan abin Alkhairi domin samun gwaggwaban lada a wajen Ubangiji.

Ya ce gidauniyar Dangote bata tsaya Kan tallafin abinci kadai ba, tana bada tallafi a Asibitoci da manyan makarantun jihar Kano.

Kazalika ya godewa shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu bisa Karin tallafin abinci da ya bawa jihar kano tallafin da

Da yake gabatar da tallafin, Alhaji Aliko Dangote yace mutane miliyan daya ne zasu amafana da tallafin buhun shinkafa gilo goma-gama daga dukkanin jihohin kasar nan baki daya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!