Connect with us

Labarai

Za mu tallafawa kamfanonin da suka durkushe a Kano – Gwamnati

Published

on

Ministan ciniki, kamfanoni da zuba jari Otunba Niyi Adebayo ya ce gwamnatin tarayya zata tallafa wajen farfado da kamfanoni da suka durkushe  a jihar Kano, kasancewar su ne ginshikai wajen bunkasa tattalin arzikin kasar nan, bayan da annubar cutar COVOID-19 ta kawo koma a wannan bangaren tattalin arzikin kasar nan.

Mr Otunba Adebayo ya bada tabbacin ne lokacin da ya kai ziyarar girmamawa ga mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero a fadar sa.

Ministan wanda ya sami wakilcin babban darakatan tsare-tsare na ma’aikatar Alhaji Tijjani Inuwa Babura ya ce sun zo Kano ne don tantance adadin kamfanonin da annubar Korona ta yi wa illa, da kuma tattaunawa da masu ruwa da tsaki don samu bakin-zaran don tallafawa masu kamfanoni a nan Kano.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 334,993 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!