Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Za mu tsayawa Abdulmalik Tanko don ya samu lauya – Barista M.A Lawal

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta tsayawa Abdulmalik Tanko wanda ake zargi da kashe ɗalibar nan Hanifah Abubakar domin ya samu lauya mai kare shi.

Kwamishinan Shari’a Barista Musa Abdullahi Lawal ne ya bayyana haka jim kaɗan bayan kammala zaman sauraron shari’ar na ranar Litinin.

“Muna neman a karantawa masu laifi tuhumar su, kuma irin wannan tuhumar babba ce dole sai yana da lauya da zai kare su”.

“Kundin tsarin mulkin Najeriya ya tilasta irin wannan tuhuma sai da lauya wannan ne ya sanya suka buƙaci lauya daga wajen mu to kuwa mun ɗauki alƙawari za mu tabbatar sun samu lauya” a cewar Barista Musa.

Kwamishinan shari’ar ya ci gaba da cewa “Mun buƙaci a ɗage shari’ar zuwa ranar 14 ga watan Fabrairu ne domin kafin lokacin za mu ba su lauya.

Barista Musa Abdullahi Lawal ya ce, da zarar an basu shaidar gwamnati a shirye ya ke ta kawo karshen shari’ar cikin hanzari.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!