Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Za mu yi duk mai yiwuwa don ceto dalibai – El-Rufai

Published

on

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce za tayi duk mai yiwuwa wajen ganin ta ceto daliban kwalejin nazarin tsirrai da dazuka ta kasa da ke Afaka, a yankin karamar hukumar Igabi da ke jihar.

A baya-bayan nan ne dai ‘yan bindiga su ka yi garkuwa da daliban su talatin da tara.

Kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro na jihar Kaduna Samuel Aruwan ne ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai.

Ya ce jami’an tsaro da suka hada da: sojoji da ‘yan sanda da jami’an hukumar tsaron sirri ta (DSS) sun dukufa suna aiki ba dare ba rana don ganin sun ceto daliban daga hannun ‘yan ta’addar.

A baya-bayan nan ne dai ‘yan bindiga suka sace daliban mata ashirin da uku da maza goma sha shida, sannan suka bukaci da a biya su kudin fansa na naira miliyan dari biyar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!