Labarai
Za mu yi duk mai yiwuwa wajen kawo karshen fadan Daba- Inuwar Kofar Mata

Kungiyar Inuwar Kofar Mata da ke jihar Kano, ta ce, za ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin an kawo karshen fadan Daba, da ake samu Musamman tsakanin Unguwannin Kofar Mata da Yakasai da kuma Zango, ta hanyar samar wa da mata da matasan yankunan ayyukan yi.
Kungiyar, ta bayyana haka ne yayin da ta ke bikin bude cibiyar koyar da matasa sana’o’in dogaro da kai ga matasa a yankin da ya gudana a Larabar makon nan.
A jawabinsa yayin taron, Shugaban Kungiyar ta Inuwar Kofar Mata, Alhaji Adamu kofar Mata, kira ya yi ga iyaye da su yi amfani da wannan dama wajen tura yayan su domin su dogara da kansu.
Shi kuwa Mai Unguwar Kofar Mata Malam Muhammad Jibrin Muhammad, ya yi fatan samar da cibiyar zai kawo karshen rashin aikin yi da shaye-shayen da matasan yankin ke fama da shi.
You must be logged in to post a comment Login