Labarai
Za muyi dokar da zata tilastawa ‘yan takara gwajin shan miyagun kwayoyi: NDLEA
Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Nijeriya NDLEA ta ce, ‘nan gaba kadan za a samar da dokar da zata tilastawa duk wani dan takara yin gwajin shan miyagun kwayoyi kafin a zabe shi.
Shugaban hukumar ta Kano Alhaji Sadik Abubakar Idris Ahmad ne ya bayyna hakan a zantawarsa da Freedom Radio da safiyar yau, wadda tattaunawar ta mayar da hankalin kan shirin yiwa yan takara gwajin shan kwayoyin maye.
Alhaji Sadik Abubakar ya ce ‘yunkurin hukumar dai ya biyo bayan kin zuwan ‘yan takarar hukumar don ayi musu gwamjin shan miyagun kwayoyi.
Shugaban hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA a nan Kano Alhaji Sadik Abubakar Idris Ahmad kenan a zantawarsa da Freedom Radio.
Rahoton:Nura Bello
You must be logged in to post a comment Login