Connect with us

Labaran Kano

Za’a kafa jami’ar noma a Kano

Published

on

Dan majalisar wakilai na tarayya Hafizu Ibrahim na mazabar Tarauni

Dan majalisar wakilai mai wakiltar karamar hukumar Tarauni a birnin Kano yace zai gabatar da kuduri a gaban majalisar domin kafa jamiar gwamnatin tarayya ta noma a jahar Kano.

Dan majalisar Hafizu Ibrahim Kawu ya bayyana haka ne lokacin shirin Barka da hantsi na nan Freedom Radio.

Hafizu Ibrahim Kawu ya kara da cewa shugaban majalisar wakilai Femi Gbajabiamila ya amince da gabatar da kudurin a gaban majalisar ta wakilai a makon da muke ciki.

Dan majalisar yace duba da yadda jahar Kano ta shahara a harkokin noma ya kamata ace ta mallaki jamiar Gwamnatin tarayya ta noma kamar yadda ake da irinta a garin Makurdin jahar Binuwai.

Yace muradin sa shi ne mayar da kwalejin koyan ayyukan gona dake unguwar Hotoro a karamar hukumar ta Tarauni jamiar gwamnatin ta tarayya anan jahar Kano.

Hafizu Kawu yace idan har kudirin ya wuce ana sa ran jamiar noman ta gwamnatin tarayya zata fara aiki a badi.

 

 

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!