Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Za’a kammala aikin layin dogo daga Legas zuwa badin – Amaechi

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ce za’a kammala aikin shimfida layin doga na jiragen kasa da ya tashi daga Lagos zuwa birnin Badin daga na zuwa watan Disamabar shekarar da muke ciki.

Ministan sufuri Rotomi Amaechi ne ya bayyana hakan lokacin da yake zantawa da manema labarai a birnin Badin babban birinin jihar Oyo.

Rotomi Ameachi ya kuma bukaci yan kwangilar da suke aikin dasu yi kokarin kammala aikin kafin nan da wa’adin da gwamnatin tarayya ta diba musu.

Tunda fari dai dan kwangilar da ke kula da aikin ya bayyanawa Ministan cewa sun sami tsaiko ne sakamakon rashin isassun Injiniyoyin da suke aikin saboda annobar cutar Covid 19 da aka fuskanta a duniya baki daya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!