Kasuwanci
Zaben shugaba Buhari ne yasa kungiyar IPOB ta rika cin mutuncin yan kasuwar Arewa.
Hadaddiyar kungiyar yan kasuwar arewacin Najeriya tace zuwan shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya saka suka kafa hadaddiyar kungiyar yan kasuwar domin magance matsalolin da ke fuskantar arewacin Najeriya da yan kasuwar su.
Mataimakin shugaban kungiyar yan kasuwa na arewacin Najeriya Jahi Abdullahi ne ya bayyana haka lokacin da yake tattaunawa da filin Barka da Hantsi na Freedom Radio.
Malam Jahi Abdullahi ya kara da cewa dalilin da yasa ake cin mutuncin nasu shugaba Buhari bayan an rantsar da shi a watan Mayun shekarar 2015.
Yace lokacin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi mulki an rika yi musu zargin da babu gaira babu dalili daga ciki har da ambatar su da sunan yan Boko haram da cin mutunci iri iri.
Jahi Abdullahi ya kara da cewa dalilin da yasa kenan suka kafa kungiyar haddaddiyar yan kasuwa ta arewacin na Najeriya inda yace a yanzu lamarin ya riga ya kau.
A sakamakon haka sai da ta kai sun ga Gwamnan jahar Abia Ikpeazu Ikeazu wanda bai ji dadin irin cin zarafin da kungiyar tabbatar da yan kasar Biafra ta IPOB ta rika yi musu ba.
Sun kuma koka da yadda baa baiwa al’ummar arewacin Najeriya damar gudanar da kasuwanci a yanayi mai kyau a yankin kudu maso gabashin Najeriya.
A nasa bangaren shugaban kungiyar ta jahar Kano Isah Haruna yace zasu cigaba da jajircewa domin taimakawa yan kasuwar jahar Kano da arewa gaba daya.