Labarai
Zaben 2023: kaso 30 na rijistar zaben yan Kano ta lalace – INEC
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta ce, sama da kaso Talatin da tara na rijistar zaben yan jihar Kano ta lalace.
Wannan dai ya biyo bayan yadda wasu suka yi rijistar ba bisa ka’ida ba.
Shugaban hukumar a nan Kano Farfesa Riskuwa Shehu Arabi ne ya bayyana hakan a ranar Talata, yayin taron tattaunawa da manema labarai na wuni guda kan yadda za su hada kai don yin aiki kafada da kafada a zaben 2023 mai karatowa.
Farfesa Riskuwa Shehu Arabi ya kuma ce “Zuwa yanzu mutanan da suka yi rijistar zabe a Kano adadin su ya kai 128,628, inda daga ciki aka samu adadin 77,255 da rijistar su ta yi kyau”.
“Domin kara saukaka yadda za a gudanar da zaben, ya sanya aka kara samar da rumfunan kada kuri’a, wanda a yanzu muna da guda 11,222” a cewar Riskuwa.
Farfesa Riskuwa Shehu Arabi ya kuma bukaci al’ummar jihar Kano da su fita domin yin rijistar zaben kafin a rufe nan da watan Yuni mai zuwa.
Ya kuma jaddada cewa hukumar za ta yi aiki kafada da kafada da manema labarai domin samun zabe ingantacce kafin da lokacin har ma da bayan zaben.
You must be logged in to post a comment Login