Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

Zaben shugabannin PDP na arewa maso yammacin Najeriya na nan -Bashir Sanata

Published

on

Jami’iyyar PDP a Kano ta musanta labarin dage zaben shugabanninta na shiyyar arewa maso yammacin kasar nan da zai gudana a ranar Asabar 12 ga Fabrairun 2022 a Jihar Kaduna.

Mai magana da yawun jami’iyyar a Kano Bashir Sanata ne ya bayyana hakan a zantwarsa da Freedom Radio.

Bashir Sanata ya ce labarin da wasu mutane ke yadawa na dage zaben da zasu gudanar a nan gaba, sam ba gaskiya ya ba ne, adon haka mambobin jami’iyyar suyi shiri namu samman domin tin karar zaben.

“Shakka babu muna ta jin cewa an dage zaben na PDP, wanda zamu iya cewa ba haka bane, kawai dai wata kuto ce ta bayar da umarnin dakatar da guda daga cikin mamba a jami’iyyar wato Bello Hayatu Gwarzo daga shiga dukanin sabgogin jami’iyyar har mada tsayawa takara a ko wacce kujera a jami’iyyar,”

“Wannan ne abin da ya faru, amma ba wai zaben da jami’iyyar zata gudanar aka dage ba, don haka muke kara tunatar da ‘yan jami’iyyar da su kara himma domin tunkarar zaben,” a cewar Bashir Sanata.

A daren ranar Alhamis ne dai aka jiwo Jam’iyyar PDP ta sanar da dakatar da babban taronta da ta shirya gudanarwa a ranar Asabar a Kaduna.

Guda daga cikin mamba a kwamitin rikon jami’iyyar shiyyar Arewa maso yamma Muhammad Akibu Dalhatu ya bayyaba, kamar yadda jaridar Nigerian Tracker ta rawaito.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!