Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Zama ya yi dadi : Amare da Kishiyoyi na kece raini a Instagaram

Published

on

A wannan makon da muke ciki ne wani sabon salon gasa tsakanin Amare da Kishiyoyi ya bullo a dandalin sada zumunta na Instagram.

Gasar wadda masu ita suka samarwa Hashtag da suna AmaryaUwarGidaChallenge kan baiwa Uwargida da Kishiya damar daukar hoton kece raini a tare, sannan su wallafa shi a dandalin na Instagram domin tabbatar da zaman lafiya a tsakanin su, inda jama’a ke fafatawa wajen zabar wadda tafi samun yawan mabiyan a tsakanin amaraya da Uwargida ta hanyar nuna sha’awa wato yin Liking a turance.

Wannan gasa dai na cigaba da daukar hankalin al’umma musamman a yankin Arewacin Najeriya da Hausawa keda rinjaye domin kuwa manyan shafukan al’ummar Hausawa musamman ma na ‘ya’ya Mata sun maida hankali kan wannan gasa.

Dandalin sada zumunta na Instagram yana da matukar tasiri ga al’umma a wannan lokaci ganin yadda al’umma suka mayar da hankali kacokan wajen bibiyarsa.

Manazartan al’amuran yau da kullum a kafafan sada zumunta na ganin cewa ana kir-kirar irin wadannan gasa da wasanni a kafafan sada zumunta ne domin cimma wasu bukatu, ko kuma samarwa mutane batutuwan tattaunawa, kasancewar ba’a zama ba tare da cece kuce ba a kafafan sada zumunta.

Kazalika an hangi manyan marubutan Hausa irin su Fauziyya D. Sulaiman da Umma Sulaiman ‘Yan Awaki wadda akafi sani da Aunty Baby na nuna farin cikin su da wannan tsari na AmaryaUwargidaChallenge inda suke ganin hakan wata hanyace da zata samar da hadin kai tsakanin ma’aurata.

Har ila yau ana samun mabanbantan ra’ayoyi game da wannan batu, domin kuwa cikin masu tsokaci akwai wadanda ke kukan cewa yanzu su da basu da Kishiya dawa zasuyi tasu gasar?

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!