Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Hukumar Hisbah ta gana da saurayin dake shirin auren Ba’amurkiya

Published

on

Hukumar Hisbah ta jihar Kano karkashin jagorancin Sheikh Harun Muhammad Sani Ibn Sina ta gana da Matashin nan Sulaiman Isah Panshekara da yake niyyar Angwancewa da wata Baturiya ‘yar Kasar Amurka.

Ganawar dai aka tsakanin hukumar ta Hisbah da wadanda suke niyyar angwancewar ya kwashe mintuna 40, a yau Asabar.

Hukumar ta Hisbah ta wallafa hakan ne a shafin ta na Facebook a dazun nan cewar ta gana da Sauranyin da kuma Amaryar sa.

Ba Amurkiya daga California ta biyo saurayinta zuwa Kano

Hisbah zata bude sabbin ofisoshi a Kano

Hisbah bata da hurumin yin bulala ko cin tara ga mai laifi -Barista Sunusi Musa

A cewar hukumar bayan da ta wallafa hotonan Saurayin Suleman Isah Panshekara da Ba’amurkiyar sun isa harabar shalkwatar hukumar ta Hisbah dake Sharada a nan Kano da yammaci.

Ku kasance da bibiyan shafun na Internet don jin yadda ganawar ta kaya.

Idan za’a iya tunawa a ranar Laraba 16 ga wannan watan da muek ciki wata Ba ‘amurkiya da ke zaune a birnin carlifonia tayo tattaki daga Amurkan bata zame ko in aba sai a unguwar Panshekara dake nan Kano, tazo takanas ta Kano domin ganawa da wani saurayin ta, dan Kano mazaunin Panshekara wanda su ka kulla abota a dandalin sada zumunta daga bisani kuma abin ya zama soyayya me karfi har takai guda baya iya runtsawa sai ya ji muryar gudan.

Tafiya dai ta yi dole karshe Baturiya Janet ta ga cewar ai gara ayi ta dungurum gum haihuwa da hanji, dan haka ta yanki tikiti ta hawo jirgi ta sauka a Panshekara, ta kuma shiga har cikin gidansu wannan saurayi na ta Suleman wanda ta ce ya gama sace zuciyar ta da kalamai na soyayya da hotunan qawa da ya ke tura mata cikin yanayin rangwada, ta kuma yi mana Karin hasken cewar, ta shirya tsaf domin daukar wannan saurayi nata domin tafiya dashi amurka a cigaba da soyewa

Suleman shi ne saurayin da tarkon sa ya kama kucciya, har takai an yo masa takakkiya daga carlfonia,zuwa gidan su dake panshekara, ya ce shima fa ya yi mata kuma kayansa su na jaka zai bi matar ta sa amma ya yi alkwarin zai dinga kawo ziyara gida

Itama Fatima Suleman mahaifiyar wannan saurayi da makota ke yiwa barka ta ce, bata da suka kan wananan alaka dan haka a tafi amurka ta amince, tun taga ita baturiyar bin tun jamilatun ce

Wani abu da shima ke jan hankali shi ne ita fa wannan ba Amurkiya shekarar ta 46 shi kuwa Suleman yaro ne sharaf mai shekaru 23,ko yaya auran zai yiwu tsakanin sa da old woman, zamu ji amsa a shirin mu na gaba.

Ku biyo cikin shirin Inda ranka don jin cikakken labarin

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!