Connect with us

Labarai

Zamfara:rundunar yan sanda ta musanta rahotannin kai hari ga shaidun Atiku Abubakar

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta musanta rahotannin da ke cewa an kai hari ga wasu shaidun dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP Atiku Abubakar.

 

 

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’in yada labaran Hukumar SP Muhammed Shehu.

 

Sanarwa ta ce babu kanshin gaskiya cikin zargin cewa an kai hari ga shaidun dan takarar jam’iyyar PDP Atiku Abubakar a jihar ta Zamfara.

 

Tun farko dai lauyan Atiku Abubakar ya shaidawa kotun sauraran korafin zaben shugaban kasa a zamanta na karshen makon jiya cewa, an kai hari ga wasu shaidun su wadanda suka bar jihar Zamfara akan hanyarsu ta zuwa Abuja.

 

Lamarin da ya sa alkalan kotun sauraran korafin zaben shugaban kasar, su ka dage ci gaba da sauraran karar zuwa wani lokaci nan gaba.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,676 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!