Connect with us

Labarai

Ma’aikatan hukumar NIPOST zasu tsunduma yajin aiki jibi

Published

on

Ma’aikatan Hukumar aikewa da wasiku ta kasa (NIPOST) sun ce za su tsunduma yajin aiki a jibi Laraba, sakamankon kin biyansu alawus din su na shekaru uku da mahukuntar hukumar su ka yi.

,

Hakan na kunshe ne cikin wata wasika da ma’aikatan su ka aikewa shugaban Hukumar na kasa Bisi Adegbuyi.

 

A cikin wasikar ma’aikatan sun ce suna gargadin Hukumar da ta biyasu alawus din nasu ko kuma su tsunduma yajin aiki a jibi laraba.

 

Wasikar mai kunshe da sa hannun shugaban kungiyar manyan ma’aikatan Hukumar Yunusa Muhammed da Sakataren kungiyar Ayo Olorunfemi, sun ce matukar hukumomin su ka gaza biyan alawus din cikin wa’adin da su ka basu, to kuwa za su tsunduma yajin aiki.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,650 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!