Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Za mu ƙara samar da Asibitin yara domin rage cinkoso a Asiya Bayero- Gwamna Abba Kabir

Published

on

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya ce, zai sake samar da wani asibitin yara a asibitin Abubakar Imam da ke Kabuga don rage cinkoson al’umma da ake fuskanta a asibitin Asiya Bayero.

Injiniya Abba Kabiru Yusuf ya bayyana hakan a daren jiya, 01 ga watan Janairun 2024 cikin wata tattaunawa ta musamman da ya gudanar da yan jarida a gidan gwamnati.

Gwamnan ya bayyana shirin da yake kan samar da asibitin domin samin sauki musamman al’ummar da suke shigowa daga yankin karkara.

Haka kuma Gwamnatin ta Yi kira ga masu hannu da shuni dama manya da kananan Ƴankasuwa dasu hada hannu da ita wajen kawo cigaban jihar.

Haka kuma Gwamna Yusuf ya ce ya zama wajibi gwamnatin sa ta hada hannu da attajiran dake Kano wajen Samar da hanyoyin farfado da masana’antun dake fadin Jihar Kano.

Ya Kuma ce hakika masana’antu na bukatar kulawa ta musamman domin farfadowa wanda hakan zai ƙara ƙarfafa kasuwanci a faɗin jihar

A ƙalla gwamnan ya shafe awanni 2 yana gudanar da jawabi da amsa tambayiyi wanda shine irin sa na farko tun bayan rantsar da shi a matsayin gwamnan Kano

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!