Labarai
Za mu ƙara haɓɓaka kasuwancin Kano
An bayyana kudurin Gwamna Abba Kabir Yusuf na gayyato masu zuba hannun Jari dan bunkasa harkokin kasuwanci a jihar Kano.
Mai bai wa Gwamnan shawara kan harkokin ma’aikatar Kasuwanci Nura Hussaini da ake yi wa lakabi da President yayin da ya ke zantawa da manema labarai a gidan sa yau Juma’a.
Nura Hussaini ya ce, ganin yadda yanzu mafi akasarin Kano a kan shigo da kayan kasuwa ne wanda babu abinda ake fitar ma da Kano matsayin suke samarwa a duniya.
Ya kara tabbatar wa al’umma cewa farfado da masana’antun da gwamnan zai yi zai taimaka matuka wajen sama wa Jama’ar Kano cigaba da ayyukan yi da bunkasa harkokin Kasuwanci a Kasa baki daya.
Sannan mai ba gwamnan Shawara kan harkokin Kasuwancin ya kara da cewa gwamna Abba Kabir mutum ne mai san mai gaskiya da rikon Amana a rayuwar sa,dan haka dole ne suma su rike masa amana tare da aiki tukuru.
Nura ya kuma kara da cewa kwanakin da gwamna yayi na farko da akafi sani da kwana 100 farko a ofis ya gabatar da ayuka daban-daban a ciki da wajen jihar Kano da ya tabbatar ya zo wa da kanawa da abin alkhairi.
Sai dai babban mashawarcin ya ce, babu abinda Gwamna Abba ke bukata a yanzu da ya wuce Addu’ar da zata taimaka masa wajen cigaba da gudanar da ayukan alkhairi ga jama’ar wannan Jiha.
“Muna san al’umma da su sani cewa dole sai an bawa gwamna dama da lokaci da zai gudanar da aiki ga al’umma, sabanin rashin uzurin da wasu basa fahimtar hakan.”
Daga karshe ya kuma yi wa Gwamnan fatan alkhairi tare da addu’ar Allah ya taimake shi wajen gudan da aikin sa cikin nutsuwa.
You must be logged in to post a comment Login