Manyan Labarai
Zamu ci gaba da feshin magani a makarantu – Ganduje
Gwamantin jihar Kano ta ce za ta ci gaba da feshin magani a makarantun jihar nan domin dai kare dalibai daga kamuwa da kwayar cutar Corona.
Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana hakan a yau lokacin da yake bude taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki dangane da shirin bude makarantu, wanda ma’aikatar ilimi ta tarayya ta shirya da hadin gwiwar hukumar bunkasa ilimi kimiyya da al’adu ta majalisar dinkin duniya UNICEF.
Gwamnan wanda ya samu wakilcin mataimakinsa Alhaji Nasir Yusuf Gawuna, ya ce dama tuni Kano ta fitar da kudi naira miliyan 880 domin gyaran makarantun a kananan hukumomi 44 na Kano.
Ya ce a yayin taron na masu ruwa da tsaki a kan harkokin ilimin za a tattauna don jin irin shirye-shiryen da a kayi dangane da komawa makarantun cikin yanayin mai kyau.
A na sa bangaren da yake jawabi karamin ministan ilimi Chukwuemeka Nwajiuba, ya ce a taron za a tattauna tare da tsara yadda za a bude makarantun cikin kariya daga kamuwa da cutar Corona.
Wakiliyarmu Zahra’u Nasir ta rawaito cewa kwamishinan ilimi na jihar Kano Muhammad Sanusi kiru ya godewa gwamnatin tarrayya bisa ga yadda take sanya hannu a kan al’amuran ilimi a nan Kano.
You must be logged in to post a comment Login