Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Zamu fitar da Naira biliyan 7 don wasu manyan ayyuka a Kano-Abba gid-gida

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta amince da fitar da naira biliyan bakwai domin gudanar da wasu manyan ayyuka a fadin jihar.

Kwamishinan yada labarai na jihar, Malam Halilu Dantiye ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai kan sakamakon taron majalisar zartarwa na mako da aka yi a Kano ranar Alhamis.

Dantiye ya ce ‘an amince da kudaden da ayyukan ne a zaman taro na biyu da na majalisar domin magance bukatun jama’a na samar da ababen more rayuwa cikin gaggawa’.

A cewarsa, ‘an bai wa ma’aikatar kasa izinin aiwatar da aikin fadada hanyar Zariya, yayin da aka baiwa ma’aikatar kimiyya da fasaha Naira miliyan 4.2 don kirkiro da tsara manufofin kimiyya, fasaha da kirkire-kirkire’.

‘Sauran hukunce-hukuncen da aka zartar sun hada da kundin tsarin mulki na kwamitin mutum 5 don duba rahoton da aka samu kan tunkarar kalubalen da amintattun asusun fansho na jihar ke fuskanta wajen aiwatar da shirin bayar da gudunmawar fansho a karkashin kwamishinan noma’.

Ya kuma bayyana cewa majalisar ta kafa kwamiti domin tantance ainihin adadin ayyukan mazabar da aka yi watsi da su da kuma ci gaba da gudana a jihar

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!