Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Zamu hukunta jami’an gwamnati da basa karbar allurar Corona – Dr Faisal Shu’ib

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ce zata dau matakin hukunta manyan jami’ai da fitattun al’umma da suka ki yadda ayi musu allurar rigakafin cutar Corona.

Babban daraktan hukumar lafiya a matakin farko na kasa Dr Faisal Shu’aibu ne ya bayyana a wata ganawa da yayi da ‘yan jaridu a birnin tarayya Abuja.

Shu’aibu yace, gwamnatin tarayya zata fito da sabbin tsare -tsare masu dauke da dokokin hukunta duk wani jami’in gwamnati da ya kaucewa kin yi musu rigakafin,kasancewar su jagororin al’umma ne da ake koyi dasu.

Babban jami’in ya kuma tabbatar da cewar kwamitin yaki da cutar Corona, na shugaban kasa zai tabbatar da cewa an samar da wadatacciyar allurar rigakafin ga al’ummar kasa, a kokarin da ake na kawar da cutar a fadin kasar nan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!