Connect with us

Labarai

Zamu hukunta masu cunkuson jama’a-FRSC

Published

on

Hukumar kiyaye abkuwar hadurra ta kasa FRSC, za ta fara kama masu cun kusa  jama’a a ababen hawa.

Hukumar kiyaye abkuwar hadurra ta kasa (FRSC), ta ce za ta fara daukan tsauraran matakai kan masu ababen hawa da ke yin lodin wuce kima.

Mai magana da yawun hukumar a nan Kano, Kabiru Ibrahim Daura ne ya bayyana haka yayin zantawa da tashar freedom rediyo.

Kabiru Ibrahim Daura, ya ce, daukar matakin ya zama wajibi domin dakile yaduwar cutar Corona wacce ta ke da saurin yaduwa a cikin al’umma ta hanayar yaduwa.

Labarai masu alaka.

Takai:Mutane 19 ne suka rasa rayukansu a wani hatsari da ya afku a kauyen Dinyar Madiga

Ganduje : za’a rufe kan iyakokin jihar Kano COVID-19

“Ko da masu baburan hawa ba a amince su dauki sama da Mutum biyu ba, ma’ana da mai tuka babur din da Kuma Mutum daya” inji Kabiru Ibrahim Daura’’.

Ya ce tun farko dama yin lodin wuce kima laifi ne, saboda haka hukumar  za ta kara sanya ido kan lamarin  domin kare lafiyar al’ummar jihar Kano dama kasa baki daya.

Wakilin mu Abdullahi Isa, ya ce hukumar ta sha alwashin yin duk mai yiwuwa wajen ganin an samu takaitar zirga zirga don dakile barzanar yaduwar cutar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Labarai

KAROTA ta kama babbar mota makare da giya

Published

on

Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano KAROTA ta ce ta chafke wata mota makare da giya da darajar kudinta ya zarta miliyan 15.

Jami’an hukumar ta KAROTA ne dai suka bi motar da ke makare da katan din giya sama da dari uku, a kan titin Zaria da misalin karfe 3 na rana bayan da driben motar ya isa yankin Unguwar Sabon gari.

 

Wannan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’in yada labarai na hukumar ta Karota Nabulisi Abubakar Kofar Na’isa, inda ta ce ko da jami’an na KAROTA suka lura direban motar hiya ya dauko ne kuma suka nemi dauki jami’an ‘yan sanda , wanda da tainakon su ne kuma suka cimma nasarar kame motar.

Direbobi sun maka KAROTA da ‘Yan sanda a gaban kotu

KAROTA ta baiwa jami’in ta kyautar kudi mai tsoka

KAROTA tayi wawan kamu a kasuwar Singa

Sai dai ya ce ko da Direban motar da sauran mutanen ciki suka lura jami’an ‘yan sanda da na KAROTA na bin su ne kuma suka tsere tare da barin motar a nan.

Sanarwar ta kuma kara da cewa duk jami’in Karotar da ya tallafawa jami’an tsaro wajen chafke mutanen da ke shigowa jihar Kano da muggan kwayoyi da kuma giya yana da kyauta mai tsoka.

Continue Reading

Labarai

Covid-19: Coronavirus ta hallaka ‘yar asalin jihar Kano a Amurka

Published

on

Annobar Coronavirus ta hallaka wata ‘yar asalin jihar Kano Hajiya Laila Abubakar Ali dake zaune a kasar Amurka.
Hajiya Laila mai shekaru sittin a duniya, ta rasu kwana daya da kamuwarta da cutar.
Mai baiwa gwamnan Kano shawara kan yada labarai Salihu Tanko Yakasai shi ne ya tabbatarwa da Freedom Radio wannan labari, inda yace marigayiyar ‘yar uwa ce ga Famanan Sakatare na ma’akatar al’amuran addini ta jihar Kano.

Karin labarai: 

Gwamnatin Kano ta musanta shigo da Corona ta Filin Jirgin saman Malam Aminu Kano

Musulmai sun yi taron addu’a kan Coronavirus a Kano

Continue Reading

Labarai

Kazafin maita ya kawo cikas ga soyayyar wasu masoya a Kano

Published

on

Soyayyar wasu matasa biyu Aliyu Tukur da Maryam Muhammad ta shiga cikin tasku bayan da dan uwan Maryam din ya yi kazafin Maita ga saurayin nata.
Wannan al’amari ya faru ne a karamar hukumar Bebeji dake nan Kano, inda Ukasha Muhammad ya rika yadawa a garin cewa saurayin kanwarsa Aliyu maye ne.
Wannan kazafi ya janyo mutanen na kyamatar Aliyu da danginsa kamar yadda ya shaidawa Freedom Radio, wanda hakan ta sanya yayi korafi ga kungiyar kare hakkin dan adam ta Human Right dake nan Kano.
Yayi wani zaman sulhu da aka gudanar jiya Laraba, Ukasha Muhammad ya nemi afuwar Aliyun a gaban mai unguwa da kuma wakilan kungiyar kare hakkin da adam.

Karin labarai:

Hukumomi sun rufe asibitin Maita a Kano

Kotu ta fara sauraron shari’ar maita a Kaduna
Shugaban kungiyar kare hakkin da adam din Karibu Yahya Lawal Kabara ya shaidawa Freedom Radio cewa, za su je can garin sannan a tara jama’a Ukashan ya zo ya kara warware maganar a gaban su.
Ita ma a nata bangaren Maryam Muhammad ta shaidawa Freedom Radio cewa, furucin dan uwanta yaso ya kawo cikas ga soyayyar su, amma a yanzu ta fahimci komai tana kuma rokon masoyin nata Aliyu da ya yafe masa, sannan soyayyar su tana nan daram za a cigaba da tsinkar fure.

Continue Reading

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 316,348 other subscribers.

Trending

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!