Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Ganduje : za’a rufe kan iyakokin jihar Kano COVID-19

Published

on

Daga ranar Juma’a 27 ga Watan Maris din nan, da karfe 12 na dare ne za a rufe duk iyakokin shigowa jihar Kano, duk cikin kokarin ko-ta-kwana na gwamnatin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje saboda neman tsari daga mummunar cutar nan ta CORONA VIRUS.

Wannan na kunshe cikin sanarwar da Sakataren Yada Labarai na Gwamnan Jihar Kano, Abba Anwar ya fitar cewar,  dukkan fasinjoji masu zuwa jihar ta bangaren zirga-zirga na cikin gida, ta filin jirgin saman Malam Aminu Kano, ba za a bar su shiga cikin garin Kanon ba, sai dai su zauna a filin jirgin saman.

A cewar sanarwar hukumomin ‘Yan Sanda da na KAROTA da na Hisbah da sauransu za su sanya ido sosai wajen ganin an yi aiki da wannan umarni.

Sannan an umarci  jama’a da su baiwa jami’ai hadin kai, da kuma bin shawarwarin jami’an kiwon lafiya don kare kai daga kamuwa daga cutar.

Kazalika ma’aikatan gwamnati da a ka ce kar su je aiki, an yi hakan ne domin su zauna a gidajensu saboda tsare kansu, da kuma jama’a su ma a na shawartarsu da  su janye jikinsu daga kasuwanni, in dai ba bisa abinda ya zama dole ba.

Daga karshe sanarwar ta kara da cewar, da wanke hannu da sabulu da ruwa da kara tsaftar muhalli ya zama wajibi a lura da su, saboda lafiyar alumma da jihar nan da kasar nan gaba daya.

Sannan a na rokon jama’a da su ci gaba da yin addu’o’in neman sauki daga Allah Mahaliccinmu.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!