Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Wani mutum ya lakadawa ma’aikaciyar asibitin Murtala duka

Published

on

Jami’an asibitin kwararru na Murtala Muhammad dake nan Kano sun tabbatar da cafke wani mutum bisa zargin ya lakadawa wata ma’aikaciyar asibitin duka.
Shugaban asibitin na Murtala Dakta Hussain Muhammad ya shaidawa Freedom Radio cewa, duk da kokarin da ma’aikatan asibitin ke yi, amma sai gashi wannan mutum da ba a bayyana sunan sa ba, ya zo ya lakadawa shugabar sashen lura da tsautsayi da agajin gaggawa dukan tsiya.
Dakta Hussain yace tuni suka mika shi hannun ‘yan sanda domin cigaba da bincike da kuma daukar matakin da ya dace.
Har ila yau shugaban asibitin na Murtala ya ce hukumar asibitin ba za su zuba idanu su bari ana cin zarafin jami’an su ba.

Karin labarai:

An raba sinadarin wanke hannu a Asibitin Murtala

Asibitin Aminu Kano ya raba maganin ciwon kunne kyauta

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!