Manyan Labarai
Zamu kafa kamfanin sifirin jiragen sama da banki mallakin jihohin arewa maso gabas – Zulum
Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya ce gwamnonin yankin arewa maso gabashin kasar nan suna shirye-shiryen kafa kamfanin jiragen sama da kuma banki mallakin al’ummar jihohin arewa maso gabas.
Farfesa Babagana Zulum ya bayyana hakan ne a jiya lokacin da ya ke jagorantar aza harsashen aikin kwaskwarimar gidan gwamnatin jihar Bauchi jim kadan bayan kammala taron gwamnonin yankin.
Ya ce burinsu shine gudanar da ayyukan raya kasa da nufin dakile matsalolin tsaro da ke addabar yankin.
Gwamnan na Borno ya kuma ce yayin taron gwamnonin sun cimma matsaya wajen kafa kamfanin jiragen sama mai suna North east Air da kuma bankin na kasuwanci wanda zai rika tallafawa ‘yan kasuwa da kuma farfado da tattalin arzikin jihohin.
A cewar sa hakan kuma na daya daga cikin dabaru na kawo karshen tarzoma da ayyukan ta’addanci da ya yi katutu a yankin.
Farfesa Babagaba Umara Zulum ya kuma yabawa takwaransa na jihar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Muhammed sakamakon ayyukan raya kasa da ya ke aiwatarwa a jihar ta Bauchi.
Gwamnan jihar ta Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Muhammed ya kara da cewa gwamnatin jihar za ta gudanar da kwaskwarimar gidan gwamnatin ne akan kudi naira biliyan shida da miliyan dari biyu.
You must be logged in to post a comment Login