Labarai
Zamu sake nazari kan yadda aka jinginar da Rumbunan adana hatsi-Nanono
Gwamnatin tarraya ta amince ta samar da hanyoyin da za’a sake yin nazari kan yadda za’a jinginar da rumbunan adana hatsi ko abinci a kasar nan ga kamfononi masu zaman kan su.
Ministan noma Alhaji Sabo Nanono ya bayyana hakan a ya yin da ya kai ziyarar gani da ido wurin rumbun adana hatsi da ya kai girman tan dubu 25 a karamar hukumar Jahun ta Jigawa.
A cewar Alhaji Sabo Nanono gwamnati zata soke lasisin duk wani kamfani da ya gaza kaiwa ga sharudan da aka gindaya wajen kula yarjejeniyar, yana mai cewar, yaje karamar hukumar ne don ganewa idanun sa yadda ake amfani da rumbunan kamar yadda aka kulla yarjejeniyar.
Nan bada jimawa za’a fara fitar da shinkafa zuwa ketare -Nanono
Za’a dawo da ma’aikatun casar Shinkafa a Kano -Nanono
Kazalika ministan ya nunar cewar, an tanadi runbunan adana kayayyakin abinci kamar su hatsi da Dawa da masara da wake da maiwa da Aca da dai sauran su a sassan kasar nan da nufin adana su don wadata kasar nan da abinci.