Labarai
Zamu samar da doka kan fitar da fatu kasashen waje-Nanono
Ministan aikin gona da raya karkara Alhaji Sabo Muhammad Nanono, ya ce, ma’aikatar aikin gona na yin kokari tare da hadin gwiwar majalisar kasa domin samar da doka da za ta haramta safarar jakai daga kasar nan.
Alhaji Sabo Muhammad Nanono ya bayyana hakan ne yayin wani taro kan kasuwancin fatun jakai da hadin gwiwar wata kungiya mai zaman kanta ta kasar Birtaniya jiya a Abuja.
Ministan wanda ya samu wakilcin babban sakataren ma’aikatar aikin gona da raya karkara, Dr. Bello Umar, ya ce, idan aka yi wannan doka, za ta taimaka gaya wajen dakile yadda ake safarar fatun jakai da wasu dabbobin da ke barazanar karewa daga doron kasa.
Za’a dawo da ma’aikatun casar Shinkafa a Kano -Nanono
Shugaban kasa ya damka Amanar biliyan 183 a hannun Kanawa
Aljhaji Sabo Nanono ya kuma ce, shakka babu fitar da fatun jakai ya karu a shekarun nan kasancewar karuwar bukatar fatun a kamfanonin magungunan kasar China.