Connect with us

Labarai

Kananan yara miliyan 12 ne ke fama da yunwa a Najeriya – Minista

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ce kimanin kananan yara milyan 12 ne ke cikin matsalar rashin wadataccen abinci.

Ma’aikatar aikin gona da raya karkara ce ta tarayya ta bayyana hakan ta bakin ministan aikin gona Alhaji Sabo Muhammad Nanono yayin zantawa da manema labarai wanda mai bashi shawara Dr. Adeyinka Onabolu ya wakilce shi, a birnin Abeokuta na jihar Ogun.

Ta cikin jawabin nasa Alhaji Sabo Nanono ya kara da cewa, tuni gwamnatin tarayya ke ci gaba da yin kokarin samar da wadataccen abinci ga kananan yara a fadin kasa baki daya.

Ya kara da cewa, kaso 37% na kananan na fama da matsalar yunwa wadda ke haifar musu da matsala ta rashin girma a sakamakon rashin wadataccen abinci mai gina jiki.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 335,289 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!