Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Zamu samar da sabon tsarin rage cinkoso a Kotu: NBA

Published

on

Kungiyar lauyoyi ta kasa NBA tace zata samar da wani sabon tsarin yiwa masu kara sulhu a wajen kotuna domin rage yawan cinkoson kararrakin da alkalai suke saurara a gabansu domin rage yawan shari’un a nan Kano.

Barista Wada Ahmad Wada ne ya bayyana haka lokacin da suka ziyarci mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero a fadar sa.

Wada Ahmad Wada yace ‘wannan tsarin zai taimakawa alkalan wajen saukaka musu yayin yanke hukunci duba da yadda shari’u sukai musu yawan’.

A nasa jawabin mai martaba sarkin kano Alhaji Aminu Ado Bayero yace ‘yaji dadin wannan tsari da kungiyoyin lauyoyi suka shigo dashi domin ta haka ne za’a magance matsalolin shari’a a  Kano, dama kasar baki daya’.

Freedom Radio ta rawaito cewa mai martaba sarkin kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya karbi Bakoncin shugabanin wasan kwallon doki ta Jihar Kano dan gabatar da shirinsu na rufe wasan kwallon doki a nan jihar kano.

Rahoton: Shamsu Da’u Abdullahi

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!