Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ranar Malamai ta Duniya:Gwamna Kano ya yaba da yadda malamai suke aikin su

Published

on

Andai ware duk ranar 5 ga watan Oktoba na ko wacce shekara a matsayin ranar malamai ta duniya

Gwamnan Jihar Kano, Alh Abba Kabir Yusuf ya yi kira ga malaman jihar da su jajirce wajen ganin sun kammala aikinsu yadda ya kamata

Wannan na zuwa ne ta cikin wata takarda da sakataren yaɗa labaran Gwamnan Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar inda Gwamna Abba Kabir Yusuf yace majalisar ɗinkin Duniya ce ta ware wannan rana domin tunawa da ranar malamai Gwamnan ya bayyana su a matsayin masu gina kasa wanda dole ne kowace gwamnati mai kishin kasa ta ba su kulawa sosai

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce ba za a iya bayyana irin gudunmawar da malamai suke bayarwa ba domin su ne mataki na farko na horar da ma’aikatan da suka daukaka a kowane fanni na ayyuka

Alh Abba Kabir ya jaddada shirye-shiryen gwamnatin sa na inganta koyo da koyarwa ta hanyar gaggauta biyan albashi, karin girma, horaswa, sake horar da malamai da sauran su domin ƙara samin ingantaccen ilimi

Ya kara da cewa, ta hanyar kwamitin sake wayar da kan al’umma (CRC), gwamnati za ta gyara ajujuwa, bandakuna da wuraren ruwa a makarantun

“Za mu karfafa tare da dorewar shirye-shiryen ciyar da makarantun firamare domin kara yawan zuwa da kuma rage illar rashin abinci mai gina jiki a Kano, wannan ko shakka babu zai inganta yanayin koyo da koyarwa a makarantunmu

A cewar Gwamnan, domin ganin an samar da ba da ilimi kyauta, an tanadi raba kayan makaranta kala biyu ga daliban makarantun firamare domin tabbatar da cewa ko wanne yaro yayi karatu cikin tsafta

Gwamnan ya yi kira ga malaman jihar da su kara kaimi tare da yin iyakacin kokarinsu domin cimma burin daukaka jihar nan ta fuskar ci gaban ilimi

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!