Labarai
Zamu yi abinda ya dace wajen isar da sakon ku- kungiyar Ma’aikatan jinya da Ungozoma
Kungiyar maikatan jinya ta jihar kano ta bayyana takaicin ta kan yadda gwamnatin kasarnan tace sai an cika wasu kaidoji masu tsauri kafin maikacin jinya ya tafi kasashen ke tare domin yin aiki.
Maikatan sun bayyana haka ne ya yin tattaki da suka gudanar a yau domin nuna kin amincewar su.
Yayin tattakin nasu zuwa sakatariyar su sun gudanar da kidade da kuma dauka Aluna wanda ke nuna ta kaicin su.
Maikatan sun bayyana cewa gwmanatin ta bayyana cewa kafin ka tafi wata kasar aiki sai an tantace ka tsawon shekaru 6 kuma sai kayi aiki shekara biyu a kasar ka.
Ma’aikatan sun kuma takaici su game da takarda da gwmanatin tarraya ta fitar inda suka ,nuna hakan a mastayin rashin adaci .
Ma’aikatan sun kuma ce Gwamnatin ta gaza kawo musu abubuwa walwala bai kamata ace ta hana su fita nema ba a wata kasar.
A yayin tattakin nasu sun kai korafin nasu ga shugaban kungiyar maikatan jinya da kuma Ungozama ta kasa rashen jihar kano Ibrahim Maikarfi Muhammad yace zasu isar da sakon nasu ga inda ya dace.
Kuma za suyi kokarin wajen gani anyi abinda ya dace kan batu.
You must be logged in to post a comment Login