Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Zamu zuba jami’an ‘yan Sanda sama da dubu biyu don duba zaben cike gurbi a Kano

Published

on

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya za ta baza jami’anta sama da dubu biyu yayin zaben cike gurbi da za a gudanar a wasu kananan hukumomin Kano a gobe Asabar.

Babban sufeton ‘yan sanda na kasa Usman
Alkali Baba ne ya tabbatar da hakan a zantawarsa da manema labarai yau juma’a.

Usman Alkali Baba wanda mataimakinsa AIG Ibrahim Sani Kaoje ya wakilta, ya gargadi ‘yan siyasa da sauran magoya bayansu, har ma da masu shirin tayar da hankali a wajen zaben, da su janye yunkurinsu don gudun fadawa komar rundunar.

Rundunar yan sandan ta Kuma yi kira ga mutane da su ba su hadin kai wajen ganin an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da lumana a gobe Asabar.

Rahoton: Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!