Connect with us

Labarai

Zan ajiye aikina idan aka tabbatar ba a yi aikin hanyar Abuja Kaduna zuwa Kano ba bisa ka’ida ba- Ministan ayyuka

Published

on

Ministan ayyuka na kasa injiniya David Umahi ya ce a shirye yake ya ajiye aikinsa idan aka tabbatar cewa aikin hanyar Abuja Kaduna Kano ba’a yi shi bisa ka’ida ba

Umahi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake kare kasafin kudin ma’aikatarsa a gaban wani Zaman hadin gwiwa na majalisar tarayya

A yayin Zaman wasu yan majalisa sun nuna damuwa kan yadda aka ba wani bangare na aikin ga wani kamfani da suka ce baiyi Suna a harkar Gina hanyoyi

Sai dai Dan majalisar Dattawa na Edo ta arewa Adams Oshiomhole ya tambayi dalilin da yasa aka Karbe aikin daga hannun wani fitaccen kamfanin gine-gine da aka sani aka baiwa kamfanin da bai yi suna sosai baba yin akin titinan.

Tunda farko dai Umahi ya soki tsarin fitar da kudaden manyan ayyuka da maiakatar kudi ta tarayya ke amfani da shi Yana mai cewa tsarin na Hana ayyukan maikatarsa ci gaba yadda ya kamata

Yayin Kare kasafin kudin Tiriliyan 3 da Biliyan 400 da aka ware wa ma’aikatarsa ya ce tsarin fitar da kudaden na yanzu na janyo tsaiko wajan aiwatar da ayyukan a cewar sa sama da Kashi 95 cikin 100 na ayyukan na Gudana don haka ana bukatar fitar da kudaden domin kammala su akan lokaci

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!