Connect with us

Labarai

Zan daure duk Bafulatani da ya kafa kungiyar tsaro a Benue – Samuel Ortom

Published

on

Gwamnan jihar Benue Samuel Ortom ya ce zai tabbatar duk wani Bafulatani makiyayi da yayi yunkurin kafa kungiyar tsaro ta Vigilante ya daure shi.

Wannan na zuwa ne biyo bayan taron manema labarai da kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore ta gudanar a birnin tarayya Abuja kan yadda za a magance matsalolin tsaro a jihar.

Sai dai a martanin sa ta bakin sakataren yada labaran sa Terver Akase, Samuel Ortom ya gargadi kungiyar Fulanin da su kada suyi gaggawar kafa rundunar tsaron Vigilante.

A cewar sa za su yi amfani da wannan damar wajen aiwatar da wasu muggan dabi’u da za su kawo rashin zaman lafiya a sassan jihar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!