Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

Gwamnati za ta tallafawa malaman makarantu masu zaman kansu

Published

on

Gwamnatin tarayya za ta fara tallafawa malaman makarantu masu zaman kansu da annobar cutar COVID-19 ta shafa.

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ne ya bayyana hakan, inda ya ce tuni Gwamnatin tarayya ta nemi manyan filaye a jihohin kasar nan 11 don gina gidaje masu dakuna biyu.

Ya kara da cewa gidajen za su zama masu saukin kudi da bai gaza milyan biyu ba.

Osinbajo ya shaida hakan ne yayin babban taron kungiyar lauyoyi ta kasa karo na sittin 60.

Mataimakin shugaban kasa na cewa Gwamnatin tarayya a baya-bayan nan ta maida hankali wajen ceto sana’oi daga rugujewa a fadin kasar nan sanadiyyar COVID-19.

Osinbajo ya bayyana cewa tattalin arzikin kasar nan na kara habaka duk kuwa da nakasu da aka samu a watannin baya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!