Manyan Labarai
Zan fara koyar da darasin Physics a makarantun Dawakin Tofa- Shugaban karamar hukuma
Shugaban karamar hukumar Dawakin Tofa Alhaji Ado Tambai Kwa yace daga zangon karatu mai kamawa zai fara koyar wa a makarantun yankin shi da ‘yan majalisar sa .
Ado Tambai Kwa ya fadi hakan ne lokacin da yake tattaunawa da filin Barka da Hantsi na nan gidan Rediyon Freedom .
Da aka tambayi Ado Tambai Kwa ko me zai koyar a zangon karatu mai kamawa yace zai iya koyar da darasin Physics tunda shi injiniya ne har ma da darasin lissafi .
Yace tun rantsar da shi a matsayin shugaban karamar hukumar Dawakin Tofa ya bayar da karfi wajen habaka ilimi a yankin.
Ado Tambai Kwa yace akwai yara da dama da ba sa iya zuwa makaranta sakamakon rashin abun hawa da kuma rashin karfi na iyayen su.
Yace hakan ce ta saka ya sayi motci guda uku masu mazauni guda hamsin domin kaiwa da dawo da yara makaranta.
A bangaren kudaden shiga kuwa yace sanda ya karbi ragamar shugabancin karamar hukumar ta Dawakin Tofa Naira dubu dari biyu da hamsin kacal suke samu amma da ya like guraran da suke zurara a yanzu suna samun kimanin Naira miliyan uku ko fiye a duk wata.