Labarai
Zan jagoranci yiwa Ali Sani Madakin Gini Kiranye- Waiya
Kwamishinan yada labarai na jihar Kano Kwamred Ibrahim Abdullahi Waiya ya ce, “Zan Jagoranci yiwa Hon. Ali Sani Madakin Gini kiranye daga Majalisar Tarayya, domin al’ummar karamar Hukumar Dala da Kano basa buƙatar wakilcinsa”.
Waiya ya bayyana hakan ne yayin taron masu ruwa da tsaki na karamar hukumar Dala da ya gudana yau Lahadi 25 ga watan Janairun shekarar 2025 a gidan Mumbayya dake gwamnaja.
Ya kuma ce karamar hukumar Dala tana bukatar jagora jajirtacce wanda zai kai matsalolin al’ummar yankin gaban majalisar wakilai dan magancewa.
Ya kuma godewa gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf bisa irin tarin mukaman da ya baiwa al’ummar karamar hukumar ta Dala.
Taron ya samu halartar shugabannin Jam’iyyar NNPP a karamar hukumar da dukkan wani mai fada a ji a siyasa da ya fito daga cikin ta.
You must be logged in to post a comment Login