Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Rundunar ‘yan sandan Kano ta gayyaci Ali Madakin Gini

Published

on

Rundunar ‘yan sandan a Jihar Kano ta gayyaci zababben dan majalisar wakilai na karamar hukumar Dala a jam’iyyar NNPP Ali Madakin Gini domin amsa wasu tambayoyi.

Ta cikin sanarwar da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan na Jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar a daren jiya Laraba, yace sun gayyaci dan majalisar ne sakamakon zargin mallakar bindiga ba bisa ka’ida ba.

https://freedomradionig.com/wp-content/uploads/2023/03/ALI-MADAKI-GUN-AN-TASHI-LAFIYA-02-03-2023.mp3?_=1

Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Tukuntawa ya ruwaito cewa ana zargin Madakin Gini ya fito da wata bindiga lokacin da ake zargin wasu gun-gun matasa sun kaiwa tawagarsa hari yayin da suke kan hanyarsu ta tarar Sanata Kwankwaso lokacin da yazo Kano domin yakin neman zabe.

Rahoton: Abdulkarim Muhammad Tukuntawa

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!