Labarai
Zan nemi takarar shugaban ƙasa a 2027 don kawo ƙarshen mulkin APC- Peter Obi

Ɗan takarar jam’iyyar Labour Party LP a zaben shekarar 2023 Peter Obi, ya ce zai nemi takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027 domin kawo ƙarshen mulkin APC.
Da ya ke magana ta cikin shirin Sunday Politics na gidan Talabijin na Channels, Peter Obi, ya ce ba su taɓa yin magana da wani ba kan cewa zai yi masa mataimaki a takarar.
Haka kuma Peter Obi ya kuma tabbatar da cewa har yanzu ɗan jam’iyyar Labour ne shi duk da cewa yana cikin jam’iyyar haɗaka ta ADC da ta ƙunshi sauran jagororin adawa da za su ƙalubalanci Shugaba Bola Tinubu na APC a 2027.
You must be logged in to post a comment Login