Labarai
Zan yi farin cikin zama gwamnan Kano – Sha’aban Sharaɗa
Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar ƙaramar hukumar birni Sha’aban Ibrahim Sharaɗa ya ce, zai yi farin ciki idan Allah ya bashi kujerar gwamna a Kano a shekarar 2023.
Sharaɗa wanda shi ne shugaban kwamitin harkokin tsaro da bayanan sirri na majalisar wakilai ne ya bayyana hakan ta cikin wata hira da ya gudanar a Freedom Radio.
Ko da aka tambaye shi kan batun tsayawar sa takara a Kano sai ya ce “Wama zalika Alallahi bi aziz”.
Cikin jawabin sa ya ce “Idan har Allah ya ba ni damar zama gwamna ina so, don ko majalisar tarayya da na nema izgilanci aka yi mun na shigeta, domin shekaru 8 baya idan aka ce zan shiga majalisar tarayya babu mai yarda”.
A batun ɓallewar su daga Jam’iyyar APC a Kano kuwa Sharaɗa ya ce “Mun tattauna mu rukunin da muke ganin akwai buƙatar a kawo sauyi a jam’iyyar APC kuma muka amince da Ahmadu Haruna Zago a matsayin shugaba”.
“Ƙarƙashin jagorancin sanata Ibrahim Shekarau mun fara ƙoƙarin dawo da martabar jam’iyyar APC.
Sharaɗa ya kuma ce “Tawagar mu ta G7 ta gudanar da zaɓe gamsasshe, amma hakan ba zai hana mu saurarar tawagar kwamitin sulhu da uwar jam’iyyar ta turo ba”.
Sha’aban Ibrahim Sharaɗa ya ce, matuƙar kotu ta ayyana Abdullahi Abbas a matsayin halastaccen shugaban jam’iyyar APC a Kano ba su da zaɓi fa ce yin biyayya.
You must be logged in to post a comment Login