Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Jamiyyar APC na shirin wargajewa – Sha’aban Sharada

Published

on

Mun fahimci APC na shirin wargajewa Sha’aban Sharada Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar Birni a nan Kano ya bayyana jam’iyyarsu ta APC na shirin wargajewa.

Mun fahimci APC na shirin wargajewa Sha’aban Sharada Dan Majalisar tarayya mai wakiltar ƙaramar hukumar Birni a nan Kano ya bayyana hakan

Ya ce” kowa yasan  jam’iyyar su tana da tarin magoya baya, wanda hakan ya sanya wasu ke shirin sake  shigowa cikinta

Amma rashin shugabanci ya hana jam’iyyar ta su samun karin magoya baya ”

” yayin gudanar da zabuka daban-daban, wanda maƘotan mu na jihohin ƙasar nan sunga abin da ya faru kuma sunyi takaici da faruwar hakan,”

“Wannan dalilin ya sa cikin jiga-jigen APC ƘarƘashin jagorancin Malam Ibrahim Shekarau  suka  tattauna domin kawo dauki a jam’iyyar tasu,” Inji Sha’aban Ibrahim Sharada.

A makon da muke ciki ne dai  wasu hotuna a shafikan sada zumunta ke yawo na wasu cikin jiga-jigan jam’iyyar APC a Kano ke shirin yiwa jam’iyyar bore a zaben shugabannin APC na matakin jihohi a mako mai zuwa.

Taron da suka gudanar a gidan tsohon gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau da ke birnin tarayya Abuja wanda ya samu halartar Sanata  Barau Jibrin, da dan majalisar tarayya  Tijjani Abdulƙadir Joɓe dake wakiltar  Dawakin Tofa ,Rimin Gado,Tofa.

Sauran sune Dan Majalisar tarayya Nasiru Abduwa Gabasawa mai wakiltar Gezawa/Gabasawa, sai ɗan majalisar tarayya Barista Haruna Dederi mai wakiltar  ƙaraye da Rogo da kuma  Sha’aban Sharada mai wakiltar ƙaramar hukumar birni sai Alhaji Shehu Ɗalhatu shugaban magoya bayan Buhari Support Group.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!