Connect with us

Labarai

Zanga-zanga ta barke a Iran bayan kisan Ayatollah

Published

on

Iraniyawa sun fantsama kan tituna inda suke gudanar da zanga-zanga tare da yin alhini bayan Amurka da Isra’ila sun kashe Jagoran Addini na ƙasar Khamenei a harin da suka kai masa.

 

Zanga-zanga ta ɓarke a yau Lahadi a faɗin ƙasar ta Iran bayan sanarwar da aka fitar cewa Amurka da Isra’ila sun kashe Jagoran Addini Ali Khamenei a hare-haren soji da suka kai ƙasar.

 

Lamarin ya jefa yankin Gabas ta Tsakiya cikin zaman zulumi kuma ya jawo kakausan martani daga cikin ƙasar.

 

Tun da farko gidan talbijin na Iran ya tabbatar da mutuwar Khamenei a hare-haren Amurka da Isra’ila, inda ya bayyana cewa Jagoran Addini na Juyin-juya-halin ya yi shahada.

 

Kazalika gwamnatin ƙasar ta sanar da makokin kwana 40 tare da bayar da hutun kwana bakwai.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!