Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Zargin almundahana: EFCC ba ta gayyaci mai ɗaki na ba – Ganduje

Published

on

Gwamnatin Kano ta musanta labarin cewa an kama mai ɗakin gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje.

Wannan na cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai Malam Muhammadu Garba ya fitar a ranar Talata.

Sanarwar ta ce ko kaɗan hukumar EFCC ba ta gayyaci mai ɗakin gwamnan ba kuma a yanzu haka ma ta na nan Kano tana ci gaba da ayyukanta.

A cewar sanarwar, abin takaici ne a ce kafafen yaɗa labarai su riƙa yaɗa irin waɗanan labaran ba tare da sun tuntubi hukumar ta EFCC ko gwamnati ba.

Tun a ranar Litinin ne dai jaridu da dama suka riƙa yaɗa labarin cewar hukumar ta EFCC ta gayyaci mai ɗakin gwamna inda ta shafe awanni suna tuhumarta.

Sai dai da safiyar Talata an gano wasu hotunan mai ɗakin gwamnan Hafsat Ganduje tare da gwamnan lokacin da suke sauka a filin tashin jirgin saman Malam Aminu Kano.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!