Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Zargin cinye kudin ƴan takara: EFCC ta fara binciken Secondus da wasu jiga-jigan PDP

Published

on

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa (EFCC) ta fara binciken shugaban jam’iyyar PDP na kasa Prince Uche Secondus kan zargin badaƙalar naira biliyan goma.

 

Rahotanni sun ce EFCC tana kuma zargin wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar waɗanda ake ganin suna da hannu wajen aikata badaƙalar

 

A cikin wani kundi da jaridar Punch ta gani a jiya talata  ya nuna cewa hukumar EFCC ta rubuta wa jagororin jam’iyyar wasika inda ta bukace su da su gurfana gabanta don amsa tambayoyi kan zargin.

 

A yau laraba ne dai ake sa ran jagororin jam’iyyar PDP din za su fara gurfana gaban hukumar ta EFCC a Abuja.

 

Tun farko dai wani jigo a jam’iyyar ta PDP Prince Kassim Afegbua shine ya rubuta wasika ga hukumar ta EFCC yana bukatar da ta binciki zargin karkatar da kudaden da ƴan takara su ka sayi form wanda ya kai jimillar naira biliyan goma.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!