Labarai
Zargin juyin mulki: Sojoji a Mali sun tsare shugaban kasa, firaminista, ministan tsaro
Rahotanni daga kasar Mali na cewa sojoji sun kama shugaban rikon kwarya na kasar Mali Bah Ndaw da firaministan kasar Moctar Ouane.
Haka zalika sojojin sun kuma kama ministan tsaron kasar Souleymane Doucoure.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa, an tsare mutanen uku ne a sansanin soji da ke Kati wani gari da ke da nisan kilomita goma sha biyar daga arewa maso yammacin birnin Bamako.
Wannan juyin mulki na zuwa ne jim kadan bayan da gwamnatin rikon kwarya na kasar ta gudanar da garambawul ga majalisar ministocin kasar.
A watan Agustan bara ne sojoji suka kifar da gwamnatin shugaba Ibrahim Boubacar Keita sakamakon rikicin siyasa da ya kaure a kasar.
You must be logged in to post a comment Login